Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A cewar rahoton kafar yada labarai ta Arham, jakadan ya bayyana cewa, matakin ba shi da nasaba da takkadamar dake tsakanin Habasha da Masar da Sudan kan katafariyar madatsar ruwan Habashar.
Ya kara da cewa, kwamishinan ofishin Jakadancin zai ci gaba da tafiyar da harkokin ofishin na tsawon lokacin dakatarwar.
A baya-bayan nan, Habasha ta rufe ofisoshin jakadancinta a kasashe da dama saboda matsalolin tattalin arziki da take fuskanta.
342/